Ban Ki Moon ya shawarci shugaba Assad

moon Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kofi Annan da Ban Ki Moon

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki Moon ya bukaci shugaban Syria, Bashar Al-Assad da ya gagguata auwatar da shirin zaman lafiyar kasar wanda wakilin majalisar, Kofi Annan ya gabatar.

Kalaman na Mista Annan sun zo ne bayan da kungiyoyin adawa a kasar suka ce dakarun gwamnati da tankokin yaki sun kaddamar da hare hare akan garin Qalaat al-Madiq da kuma wasu kauyuka dake kusa da lardin Hama.

Wannan bukatar ta Mista Ban ta zo ne bayan da Kwamishiniyar Majalisar dinkin duniya mai kula da Hakkokin bil Adama, Navi Pillay ta zargi shugaba Bashar al Assad da hannu dumu-dumu a zub da jinin al'ummar kasar ta Syria.

Navi Pillay dai ta ce an aikata abubuwa da dama na cin zarafin bil-Adama ana ma ci gaba da aikatawa, kuma a matsayinsa na hafsan hasoshin rundunonin sojin kasar, Shugaba Bashar al Assad zai iya ba da umarnin dakatar da zub da jini in ya ga dama.

Ms Pillay ta zargi hukumomin kasar ta Syria tsare kananan yara da gangan.

Ta ce "idan aka yi la'akari da cewa hukumomin tsaro da na leken asiri suna karbar umurni ne kai-tsaye daga Shugaba Assad, to babu shakka zai iya ba da umurni daya a saki dukkan yaran da aka kama don su koma gaban iyayensu, a kuma saki mutanen da ke tsare a kuma daina zub da jini".

Wadannan kalamai na Ms Pillay na zuwa ne dai kwana guda bayan da mai magana da yawun wakilin Majalisar dinkin duniya da Kungiyar Kasashen Larabaw na Musamman, Kofi Annan, ya bayyana cewa kasar ta Syria ta amince da shirin samar da zaman lafiyar da Mista Annan ya gabatar mata, al'amarin da ya sa wasu ke ganin Majalisar dinkin duniya tana baki biyu.

'Bukatun da Kofi Annan ya gabatar'

Shirin samar da zaman lafiyar dai ya tanadi Majalisar dinkin duniya ta sa ido a kan matakan kawo karshen tashe-tashen hankula, da janye dakarun gwamnati daga biranen da ke hannun 'yan tawaye, da kuma baiwa ma'aikatan agaji damar shiga.

Kungiyoyin 'yan adawar kasar ta Syria dai, wadanda ke wani taro a kasar Turkiyya, sun nuna shakku da amincewar Shugaba Assad da shirin zaman lafiyar.

Akasarin kungiyoyin 'yan adawar da ke halartar taron dai sun amince da bayyana Majalisar Kasa ta Syria, Syrian National council, a matsayin hukumar da ke wakiltar al'ummar kasar.

Daya daga cikin shugabannin majalisar, Bassma Kodmani, ta shaidawa BBC cewa hakan wani muhimmin ci gaba ne ga 'yan adawar:

Ta ce "muna bukatar karfafa gwiwar kasashen duniya masu sha'awar taimakawa juyin-juya-hali na Syria cewa wannan ce kungiyar da za ta iya karkata kayan agaji zuwa ga al'ummar da ke cikin Syria".

Kodmani ta kara da cewar "ina ganin kuma mun cimma wannan burin. Majalisar Kasa ta Syriar tana da kafofin tallafawa al'umma don su ci gaba da gwagwarmaya".

Karin bayani