Kasashen BRICS za su kafa bankinsu na kansu

Shugabannin kasashen BRICS Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugabannin kasashen BRICS

Shugabanni daga kasashe biyar na duniya wadanda tattalin arzikinsu ke habaka sun kawo shawarar kafa wani bankin raya kasashen na hadin guiwa wanda suke fatan zai yi gogayya da Bankin Duniya.

Yayin wani taro a Delhi, wakilai daga kasashen Brazil da Rasha da India da China da kuma Afirka ta Kudu—BRICS—sun amince su kara kusantar juna ta hanyar kasuwanci da alakar kudade da kuma rage dogaro da Turai da Arewacin Amurka.

Kungiyar tana da kashi ashirin da takwas cikin dari na tattalin arzikin duniya.

Da yake magana a kan yanayin da ake ciki a Syria da Gabas ta Tsakiya, Firayim Ministan India, Manmohan Singh, ya yi gargadi game da daukar matakan da za su iya kawo cikas ga kasuwar makamashi da cinikayya a duniya:

“Dole ne mu kaucewa katsalandan na siyasa wanda zai iya haddasa tangal-tangal a kasuwannin makamashi na duniya sannan kuma ya shafi gudanar kasuwanci”.