Shugabannin ECOWAS sun kasa sauka a Mali

Kadre Desire Ouedraogo da Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban hukumar ECOWAS, Kadre Desire Ouedraogo da Shugaba Alassane Ouattara

A yau ne aka shirya wata tawagar shugabannin kasashen Yammacin Afirka a karkashin inuwar kungiyar ECOWAS za su kai ziyara zuwa kasar Mali don tattaunawa da shugabannin mulkin sojan kasar don ganin an maidoda mulkin farar hula a kasar.

Sai dai kuma tawagar ta juya zuwa Abidjan bayan da ta samu labarin cewa wadansu mutane suna gudanar da zanga-zanga a filin saukar jiragen sama na Bamako.

Shugaban ECOWAS, Alassane Ouattara na Ivory Coast ne ke shugabantar tawagar wacce ta kunshi shugabannin Najeriya, da Nijar, da Benin, da Liberia, da kuma Burkina Faso.

Kungiyar ta ECOWAS dai tana ganin cewa sasantawa ce mafita ga irin matsalar da aka shiga a kasar ta Mali.

Karin bayani