Batun Syria zai mamaye taron Larabawa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Assad

Ana tsammanin rikicin Syria zai mamaye tattaunawar da za a yi a taron Koli na Kungiyar kasashen Larabawa da ake yi a Iraqi.

a ranar jajiberin taron dai Kasar Amurka ta zargi shugaban Kasar Syrian, Bashar al Assad da karya alkawarin amincewa da dabtarin samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar kasashen Larabawa suka zartar.

Batun rikicin Syria dai shine babban makasudin yin taron na kasashen Larabawa inda tsohon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan zai yiwa shugabannin kasashen jawabi.

Majalisar dinkin duniya ta futar da kididdiga da ta nuna cewar akalla mutane dubu tara sun rasu kawo yanzu a fadan na Syria inda gwamnatin take kokarin dankwafe masu adawa da gwamnatin shugaba Assad.

Duk da cewa dai kungiyar kasashen larabawan ta kori Syria daga kungiyar amma kungiyar ta mika wuya ga yunkurin da mai shiga tsakanin na kasa da kasa, Kofi Annan yakeyi don kawo karshen rikicin.

Ba dai a tsammanin wata gagarumar nasara a taron a bangaren Syria ko kuma tashin hankali tsakanin yan Shi'ah da yan sunni a yankin. Wannan shine taron Kungiyar na farko a kasar tun lokacin da gwamnatin saddam Hussaini ta shude.

Karin bayani