Najeriya ta soma gina tsangaya 400

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta soma gina wasu makarantun 400 a jahohi goma sha tara na arewacin kasar, da manufar shigar da karantun almajirci cikin tsarin karatu na hukuma.

Wannan matakin a cewar gwamnatin wani yunkuri na magance matsalar yawon barace-baracen da almajiran ke yi, da kuma baiwa dubban yaran damar samun ingantaccen ilmi.

Sai dai wasu masu fashin baki na ganin cewar gwamnatin na son ta sanya hannu cikin sha'anin almajircin ne saboda tunanin cewar a makarantun almajiran ne wasu masu tada kayar- baya a kasar ke koyon tsananin kishin addini.

Dr Sulaiman Khalid malamin koyarda zamantakewar dan Adam a Jami'ar Dan fodio dake Sakkwato ya shaidawa BBc cewa, galibi gwamnatoci na futo da irin wannnan mataki yayinda wani rikici ya faru kan addini.

Ya ce ko lokacin da akayi fadan maitatsine wasu gwamnatocin Jihohi sun futoda dokokin rage yawan zurga-zurgar almajirai.

Kafin zuwan karatun Boko dai karatun allo ne akeyi a yankin Arewacin kasar wanda ya haifar da rubutun ajami.

Karin bayani