Burtaniya za ta tallafawa yan adawar Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption wasu 'yan Syria sun ji rauni

Burtaniya za ta ninka agajin da ba na karfin soji ba, da take baiwa 'yan adawar gwamnatin Shugaba Assad a Syria.

Ministan harkokin wajen Burtaniya William Hague, ya ce ka rin wasu rabin pam miliyan daya, zai taimakawa kungiyoyin da ake murkushewa a Syria, da ma na wajen kasar.

Mr Hague ya kuma ce Shugaba Assad ya kwana da sanin cewa ba shi da tabbacin mulkinsa zai dore.

Sai dai wannan matsayi na Burtaniya ya zo ne a daidai lokacin da Kofin Anan ke yunkurin wanzarda zaman lafiya a Syria.

Mr Hague ya ja kunnen gwmanatin Syria kan amfani da tashin hankali abu ne da ba za ta iya kare kanta ba; abu ne kuma inji shi mai muni.

Karin bayani