'Yan sandan Faransa sun kama mutane 19

Samamen da 'yan sandan Faransa suka kai Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan Faransa sun kama mutane da dama

'Yan sandan Faransa sun kama wasu mutane goma sha tara wadanda ake zargin masu kishin Islama ne a wani samame a ko'ina cikin kasar ta Faransa—kuma Shugaba Nicolas Sarkozy ya ce za a kara kai wadansu samamen.

"Suna da alaka da wani nau'i na tsatstsauran kishin Islama, kuma [samamen] na kan cikakkiyar hanyar doka", in ji Shugaba Sarkozy.

Galibin kamen na ranar Juma'a dai an yi su ne a kudu masu yammacin birnin Toulouse—gidan dan bindigar nan Mohammed Merah, wanda ya kashe mutane bakwai a hare-hare uku daban-daban.

Daya daga cikin wadanda aka tsare shugaban wata kungiyar masu tsatstsauran kishin Islama ne wadda aka haramta, Forsane Alizza.

An dai bayar da rahoton cewa Mohammed Merah yana da alaka da kungiyar.

Karin bayani