Mutane 18 sun mutu a hadarin mota a Kaduna

Wani hadarin mota a Najeriya
Image caption Wani hadarin mota a Najeriya

Mutane goma sha takwas sun riga mu gidan gaskiya, wadansu sama da hamsin kuma sun samu munanan raunuka a wani hadarin mota da ya auku a Birnin Bwari a jahar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Bayanai dai sun nuna cewa wata motar daukar siminti ce dauke da mutane dari da goma sha tara ta kwace ta kuma kife yayin da ake zaton direban motar ke cikin maye.

An kuma bayar da rahoton cewa motar, wacce ta wani babban kamfani ce, ta sauke lodin simintin ne a Kano, sannan ta debo fasinjoji da nufin kai su Lagos.

Balaguro a motocin kaya a Najeriya dai ya zama wata babbar hanya ta asarar rayuka, inda wani zubi irin wadannan motoci kan yi watsi da fasinjojinsu yayin da suke sukwanar gudu.

Karin bayani