Shugabannin Mali na fama da matsin lamba

Sojan Mali Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojan Mali

Ana cigaba da matsin lamba ta fuskar soja da diplomasiyya akan bjirarrun sojan Mali da suka yi juyin mulki.

Yanzu haka dai 'yan tawayen Azbinawa sun kwace iko da garin Kidal dake arewacin kasar bayan dakarun gwamnatin Mali sun tsere sun bar wuraren da suke iko da su.

Tuni dai shugaban masu juyin mulkin, Kaftin Amadou Sanogo ya maida martani ga kwace iko da garin Kidal da yin kira ga kasashen duniya su taimaka wajen kare kasar Mali.

Sai dai kuma jim kadan da aukuwar hakan, shugabannin mulkin sojan Malin sun fuskanci karin koma baya yayin da aka dakatar da kasar daga cikin kungiyar kasashen Afurka rainon Faransa.

Karin bayani