ECOWAS ta bawa gwamnatin Sojin Mali wa'adi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojin Mali a Bamako

Shugbannin Afrika ta Yamma sun baiwa sojojin da suka yi juyin mulki a Mali wa'adi zuwa ranar litinin da su dawo da turbar Demokradiyya, gami da kundin tsarin mulkin kasar, ko kuma su fuskanci ta kunkumi.

Shugabannin sun ce za su rufe iyakokin Malin, sannan su rufe asusun Kasar a Babban bankin yankin.

Shugabannin dai sun sake shawarar su gana a Ivory Coast, yayinda masu marawa juyin mulkin baya suka mamaye filin jirgin da zasu sauka a birnin Bamako.

sojojin da sukayi juyin mulkin dai a Mali makon da ya gabata za su fuskanci ta kunkumi mai tsaurin gaske matsawar ba su bi umarnin Shugabannin kasashen Yammacin Afrikan ba, cewa su dawo da kundin tsarin mulkin kasar da shauran turbar dimokradiyya.

Sai dai wasu yan kasar sun nuna goyon bayansu karara ga mulkin sojin bayanda suka mamaye filin saukar jiragen saman kasar na Bamako don hana shugabannin Afrika ta yamman sauka

Karin bayani