Ana gudanar da zaben Gwamna a Kebbi

Image caption Attahiru Jega

A yau ne ake gudanar da sabon zaben Gwamna a jahar Kebbi, bayan soke zaben gwamnan Jihar da kotun kolin kasar tayi a watan jiya.

Sai dai ana yiwa zaben kallon cikon umarni ne kawai, domin dan takarar jam'iyya mai mulki ne kawai zai shiga zaben, saboda 'yan takarar manyan jam'iyyun adawa sun janye daga shiga zaben.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ce ta shirya tsaf don gudanar da zaben a Jihar dake arewa maso yammacin Najeriya.

Shugaba Good luck Jonathan ya ce zaben wata dama ce da yan Najeriya dama wasu yan kasashen ketare za suyi nazari kan zaben da za ayi a Kebbin.