Mali: soja zasu dawo da tsarin mulki

Kaftin Amadou Sonogo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kaftin Amadou Sonogo

Sojojin da suka jagoranci juyin mulki a kasar Mali sun ce daga yau zasu dawo da aiki da kundin tsarin mulkin kasar, da ma sauran cibiyoyin mulkin kasar.

Wakilin BC ya ce, sanarwar hakan na zuwa yayin da wadanda suka kifar da gwamnatin ke fuskantar matsananciyar matsin lamba daga sauran kasashen Afrika ta yamma, wadanda suka yi barazanar sa wa kasar ta Mali takunkumin karya tattalin arziki nan da sha biyun daren yau.

Kafin haka dai an bada rahotanin cewa, dakarun kasar ta Mali sun tsere daga garin Timbuktu dake cikin hamada. Dakarun Azbinawa 'yan tawaye sun yi ma birnin kofar rago, kuma nan ne sansanin soja na karshe da ya rage a arewacin kasar.

Karin bayani