'Yan Tawayen Mali sun kwace Gao

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Amadou Sanogo

Yan tawayen kasar Mali sun kwa ce birnin Gao, gami da wani babban sansanin sojin dake yankin arewacin kasar.

Shugaban sojin da suka kwa ce mulki a juyin mulki makon da ya gabata, Amadou Sanogo, ya ce sojojinsa sun sakarwa yan tawayen birnin ne saboda gudun lalata inda gidajen jamaa suke.

Wannan dai wani ci baya ne ga masu juyin mulkin wanda suka habbarar da shugaban kasar saboda korafi kan sakaci wajan yakar yan tawayen.

ECOWAS dai tuni sun wa re sojoji dubu biyu don shirin ko ta kwana ko akwai yiwuwar kawo dauki a Malin.

Karin bayani