Mazauna Kogin Komadugu na cikin damuwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan

A Najeriya, al'umomin dake yankin kogin Komadugu-Yobe wanda ya ratsa jihohin Yobe da Bauchi da kuma Jigawa na cikin wani mawuyacin halina.

Mutanen dake zaune a yankunan galibinsu manoma da masunta na ci gaba da kokawa saboda yadda rashin gyaran kogin ke illa ga rayuwarsu ta fuskar tattalin arziki da kuma zamantakewa.

Ko wanne dai da irin ta sa matsalar, a Jigawa dai yawan ambaliyar ruwa ne sakamakon cushewar kogin ke addabar mazauna yankunan.

A jihohin Bauchi da Yobe kuwa karancin ruwan kogin ne ke hana su damar gudanar da harkokinsu.

Ana dai zargin hukumomi a Najeriyar da rashin maida himma kamar yadda ya kamata wajen alkinta kogin, lamarin da ya sanya kungiyoyi masu zaman kansu da dama ke bada ta su gudummawa.

Karin bayani