Wakilan kasashe 70 ne za su hadu a Istanbul

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ban ki-Moon

Wakilan sama da kasashe saba'in ne za su hadu a Istanbul a yau idan an jima don tattaunawa kan hanyoyin kara matsin lamba ga shugaba Bashar al Assad.

Jigon masu adawa da gwamnatin Syrian na kira da a taimakwa masu boren da makamai, abunda wasu kasashen Larabawa suka marawa hakan baya.

Amma dai galibin kasashen da suke halartar taron na tsoron ambaliyar makaman zuwa kasar ka iya kawo yaki tsakanin mabiya dariku daban daban.

Sai dai a maimakon haka suna ganin za su durfafi hanyoyin da zai sa shugaba Assad ya aiwatarda tsarin wanzarda zaman lafiya da Kofi Anan ke kokarin yi.

Karin bayani