Ana murnar nasarar jam'iyyar NLD a Burma

Aung San Suu Kyi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aung San Suu Kyi

Jagorar 'yan adawa a Burma, Aung San Suu Kyi, ta ce jam'iyyarta ta samu gagarumar nasara a zaben da aka gudanar na cike gurbi, a kasar.

Ms Suu Kyi ta ce tana fata nasarar zata bude wani sabon babi a kasar.

Jami'iyyarta ta National League for Democracy ta samu nasara a a kalla mazabu 43 cikin mazabu 44 din da ta yi takara a cikinsu.

Amma kuma yawan kujerun da ta samu bai taka kara ya karya ba a majalisar dokokin kasar, kuma a hukumance, har yanzu ba a bayyana sakamakon zaben ba.

Magoya bayan Aung San Suu Kyi sun yi dafifi a hedkwatar jam'iyyarta dake birnin Rangoon inda suke ta shagulgulan samun nasara.

Masu aiko da rahotanni sun ce jam'iyyar dake mulki wadda ke da goyan bayan sojoji za tai matukar girgiza da kayen da ta sha, musamman a mazabun da ake da ma'aikatan gwamnati da dama.