ECOWAS ta kakabawa Mali takunkumi

Shugabannin kungiyar ECOWAS Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugabannin kungiyar ECOWAS

Kungiyar raya tattalin arzukin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ko CEDEAO ta kakabawa Mali takunkumin tattalin arzuki da na diplomasiyya, saboda juyin mulkin da aka yii kwanaki goman da suka gabata.

Yanzu haka an rufe kan iyakokin kasar ta mali, an kuma hana bankin yankin yin hulda da kasar.

Shugabannin kasashen yammacin Afirka dake taro a Dakar, babban birnin Senegal sun ce takunkumin zai ci gaba da aiki har sai an dawo da bin doka da oda kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadar.

Karin bayani