Sa-in-sa tsakanin Sudan da Sudan ta kudu

Sojoji Sudan ta kudu a kan wani tanki yaki da su ka kona

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sojoji Sudan ta kudu a kan wani tanki yaki da su ka kona

Kasar Sudan da Sudan ta kudu na zargin juna da rura rikicin iyaka da ke tsakanin kasashen biyu a yanzu haka.

Sojin kasashen biyu dai na fafatawa ne a kan iyakokin yunkunan da a ke takkadama akansu a makon daya gabata.

Hakan kuma ya katse tattaunawar sulhu da kasashen ke yi a makwabciyar ta Habasaha.

Kasashen biyu dai na zargin juna ne da keta dokar kasa da kasa.

Kasar Sudan dai ta ce sojojin Sudan ta kudu ne suka kai mata hari a kusan da garin hakar mai na Heglig, wanda a dokar kasa da kasa ke karkashin Sudan din.

Martani

Sojojin Sudan kuma sunce suna maida martani ne daga mahara.

A ranar Litininan din da ta gabata ne dai Sojojin Sudan ta kudu su ka yunkuro zuwa garin na Heglig, abun da kuma ya haddasa fito na fito a karon farko tsakanin kasashen biyu tun bayan da Sudan ta kudu ta samu gashin kanta a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Sabbin shugabanin kasar dai sun musanta cewa su ne suka fara kai hari.

A jiya ma, sai da su ka zargin sojojin Sudan da kai musu hare-hare ta sama a wasu yankunansu .

Mai magana da yawun sojin Sudan ta kudu ya ce sojin kasar sun kare kansu da kuma maida martani a lokacin da aka kai musu hare-hare a jihar Unity.

Yankunan da ake rikicin dai ba su da nisa tsakaninsu, kuma suna kan iyakokin da ake takkadama ne a kansu.

Rikicin dai ake yi tsakanin kasashen biyu dai ya jefa shirin sulhu cikin wani mawuyacin hali.