Masu kishin Islama na barazana: Inji Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kama masu kishin Islama a Faransa

Mai shigar da kara na birnin Paris ya ce zai bukaci a tuhumi masu tsattsauran ra'ayin addinin Islaman nan 13 da aka kama ranar Juma'a da laifin ta'addanci.

Francois Molins ya kuma ce ana zargin mutanen da yunkurin sace wasu mutane ciki har da alkalin kotun majistare na Lyon.

Alkalin mai suna Albert Levy ne ya jagoranci sauraron wata kara inda aka yankewa daya daga cikin mutanen da aka kama din hukunci shekaru biyu da suka gabata.

Ministan cikin gida na Faransa Claude Gueant ya ce mutanen suna barazana ga al'ummar kasar.

Ya ce mutanen nan sun furta kalaman da ke rura wutar kiyayya, da tashin hankali, sannan kuma akalla daya daga cikinsu ya aikata abubuwan da ke barazana ga tsaron al'ummar Faransa

Karin bayani