Dan bindiga ya harbe mutane 7 a birnin Oakland

Hakkin mallakar hoto Other

Wani dan bindiga ya bude wuta a wata karamar Kwaleji mai zaman kan ta dake birnin Oakland a jihar California na kasar Amurka inda ya kashe mutane 7 da kuma jikkata mutane ukku.

Babban jami'in 'yan sanda na yankin ya ce mutumin da ake zargi mai suna One Goh dan shekaru arba'in da ukku da haihuwa tsohon dalibi ne a Kwalejin.

Ya ce dan bindiga daadin wanda daga bisani ya mika kansa ga 'yan sanda a wata cibiyar hada-hadar kasuwanci, ya bude wuta ne a cikin aji kafin ya fara harbin sauran wasu wurare a cikin ginin.

Wasu mutanen da suka shaida lamarin sun bayyana abinda suka gani:

Ya ce; "Na ga kawai 'yan sanda sun dauko wasu gawarwaki daga cikin ginin.

"Na gan su sun dauko gawar wani, inda suka rufe shi da bargo."

Kwalejin mai suna Jaami'ar Oikos, akasari ta 'yan kasar Korea ce, kuma tana horad da dalibai ne darussan aikin jinya, da addini da magunguna na mutanen.