Karuwar yaran da ke kamuwa da cutar polio a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP

A yau ne ake sa ran hukumomin lafiya a Najeriya ke kamala zagaye na biyu na rigakafin cutar Shan inna na wannan shekara da aka soma a karshen mako.

Sai dai wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar yaran da ke kamuwa da cutar a kasar inda daga farkon wannan shekarar zuwa yau aka samu yara goma sha hudu da suka kamu da cutar a jihohi daban-daban na arewacin kasar.

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen duniya uku da suka rage da cutar ta sha inna a duniya bayaga kasashen , Pakistan da kuma Afghanistan.

A cewar Hukumar kiwo lafiya a matakin farko ta kasar dai tana fatan kararda digon maganin riga kafin miliyan 65 da dubu 126 data keben domin yiwa yaran kasar 'yan kasa ga shekaru biyar miliyan hamsin rigakafin cutar mai gurgunta yara har karshen rayuwarsu.

Sai dai kuma matsalar rashin amincewar iyaye ga yiwa yaransu rigakafin wadda itace hukumomin kasar ke ganin ta haifar da sake dawowar cutar a kasar.

Ko baya ga rashin yardar a wasu lokuttan malaman rigakafin kan fuskaci barazanar duka a wasu gidajen a cewar wani mai unguwa a Sakkwato Malam Muhammadu Murtala dake raka masu rigakafin domin gamsar da iyaye su amince da a yiwa yaransu rigakafin.

Wuri na karshe da aka samu bullar cutar ta Sha' inna kafin somawar wannan shirin shine garin Birnin Gwari dake jihar Kaduna a arewa maso yammacin kasar.