Al Qaeda na kulla kawance da kungiyoyin Afrika

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Mayakan Al-qaeda

Wani rahoto da kwararru suka bayar daga Royal United Services Institute dake London ya ce Kungiyar masu tsattsauran ra'ayin nan ta musulmi al-qaeda wadda a yanzu Shugabancin ta ya yi rauni, tana neman kungiyoyin da za ta hada karfi da su a nahiyar Afrika ta yadda za ta sake dawo da karfin ta.

Rahoton yace, al-qaeda tana cigaba kakkafawa da kuma ingiza kungiyoyin musulmi na kasashen Afrika a kokarin bude wani sabon fage na yunkurin da take na kaddamar da jihadi a duniya.

Rahoton ya ce, al-qaeda tana ci gaba kakkafa da kuma ingiza kungiyoyin musulmi na kasashen Afrika a kokarin bude wani sabon fage na yunkurin da take na kaddamar da jihadi a duniya.

Rahoton ya yi tsokaci game da batun tashin hankalin da ake fama da shi a sassa dabam-dabam na nahiyar daga kasar Mali a Yammaci zuwa Nijer da Nijeriya da kuma kasashen Somalia da kuma gabashin kusarwar Afrika.

Rahoton ya ce Al Qaeda na amfani damar gibin da ake samu na shugabanci a wasu kasashen Afrika domin kulla dangataka da kungiyoyin Islama a wannan yanki. Hakan ya riga ya faru a kasar Somalia, inda kungiyar Al shabab ke da iko a garuruwan da dama kuma ta hada gwiwa da kungiyar al qaeda a yankin maghrib wadda ke taimaka mata da mayaka.

Rahoton ya kara da cewa kungiyar Al Qaeda na taimakon kungiyoyin islama masu tsautsauran ra'ayi da makamai da kuma kudi a nahiyar.

Har wa yau ya ce kungiyar Boko Haram a Najeriya na da alaka da al qa'eda gane irin salon hare-haren da ta ke kaiwa masu muni.

Cibiyar Royal United Services dai ta ce habbakar irin wadannan kungiyoyi a Afrika na iya kaiwa ga Burtaniya musamman ma a al'ummar 'yan Somalia da ke zaune a kasar.