ANC ta kori Julius Malema

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Majalisar zartarwar jam'iyar ANC ta Afrika ta Kudu ta cire shugaban reshen matasanta, Julius Malema daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.

Kwamitin da'ar jami'yar ANC din ya kuma haramtawa Mista Malema halartar duk wani taro na jami'yar, bayan Malema din ya bayyana shugaba Jacob Zuma a matsayin mai mulkin kama karya.

Tun a watan Fabrairu ne aka kori Mista Malema a jamiyar ta ANC amma kuma aka barshi da mukaminsa tare da damar halartar tarukan jam'iyyar, har sai an saurari daukaka karar da yayi nan gaba a cikin wannan watan.