Kungiyar Tarrayar Afrika ta sanyawa Mali takunkumi

Hakkin mallakar hoto

Kungiyar hada kan kasashen Afrika watau AU ta ba da sanarwa cewar ta garkama wa sabbin Shugabannin mulkin Soji a kasar Mali takunkumi da kuma kungiyoyin 'yan tawayen da suka kwace ikon mulki da yankin arewacin kasar.

Matakan da kungiyar ta dauka sun hada da haramcin tafiye-tafiye da kuma kwace kadarorin Captain Amadou Sanogo wanda ya jagorancin juyin mulkin.

Takunkumin doriya ne a kan jerin takunkumin da kungiyar raaya tattalin arzikin Afrika ta yamma ne ECOWAS ta saka ma kasar ta Mali a ranar litinin.

To sai dai maimakon mika ragamar mulkin, jagoran sojojin kyaftin Sanogo ya sake nanata tayin da ya yi na tattaunawa a kan shirin maida mulkin kasar ga farar hula.

Ya ce; "Muna gayyatar 'yan siyasa da wakilan jama'ar kasa su zo taron kasa da za a fara ranar alhamis don 'yan kasar Mali su yanke shawara a kan abinda ya fi zama mafi a'ala ga kasar cikin lumana,democradiyya da 'yanci."