Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwa a kan Alka'ida a Mali

Sojin Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin sojin na cikin tsaka mai wuya

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwa a kan kasancewar kungiyar Alka'ida a arewacin Mali sakamakon juyin mulkin da aka yi a kasar.

A cewar kwamitin, hakan zai kara tabarbarar da tsaro a kasar.

Kwamitin kuma ya yi Allah wadai da 'yan tawayen a arewacin kasar, wadanda suka mamaye kusan rabin kasar.

Har ila yau, kwamitin ya nuna goyon baya a kan tukunkumin da kungiyar tarrayar Afrika, AU, da kuma Kungiyar Tattalin Arziki ta Kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS, suka kakaba wa kasar ta Mali.

Amma kuma jakadan Mali a Majalisar Dinkin Duniya, Oumar Daou, ya ce kasar na cikin yanayi marar dadi.

Ya ce, “A yau Mali na bukatar taimakon kasashen duniya, wannan ne karon farko da muka tsinci kanmu a wannan yanayin.

Ba mu taba fuskantar irin wannan matsalar ba.

Karin bayani