An yi kira a tsige Shugaba Jonathan bisa zargin cin hanci

A Najeriya fadar shugaban kasar ta yi Allah wadai da kiran da jam'iyyar adawa ta ACN ta yi ga majalisar dokokin kasar na ta tsige shugaba Goodluck Jonathan.

Ta yi kiran ne a kan zargin cewa Shugaba Jonathan din ya karbi toshiyar baki daga wani kamfanin gine-gine ta wata katafariyar coci da kamfanin ya gina a garin shugban.

A nata bangaren, jam'iyyar PDP ta shugaban kasar ta zargi ACN din da yunkurin tada rikicin addini kan lamarin.

Najeriyar dai tana cikin kasashen na gaba-gaba a duniya a kan cin hanci da rashawa.

Ba da na goro kuma yana neman zama al’ada a kasar.

Karin bayani