Amurka ta sausautawa Burma takunkumi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta bayyana karin sausaucin takunkumi da Amurka ta kakkabawa Burma.

Mises Clinton ta ce Amurka ta dauki matakin ne saboda nasarar da aka samu a zaben cike gurabu da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata a kasar.

Tuni dai, Hilary Clinton ta bayyana cewa Amurka za ta dauki matakan da za su inganta harkar demokradiyya a kasar ta Burma.

A lokacin da tsohuwar fursanar siyasa Aung San Suu Kyi ta yi nasara a zaben 'yan Majalisu, masu lurra da al'amura sun yi hasashen cewa Amurka za ta dauki mataki a kasar.

Amurka dai ta dage wasu daga cikin takunkumin harkar zurga zurga da ta kakkabawa kasar, sanar manyan jami'an gwamnatin kasar za su iya ziyartar Amurka a yayinda ita kuma Amurka za ta bude Ofishin ayyukan ci gaba a Burma.

Sauyi

Hillary Clinton dai ta ce sakamakon zaben da aka gudanar a ranar daya ga watan Afrailu na cike gurabu a Majalisa ya nuna karara cewa gwamnatin kasar na aiwatar da gaggaruwar sauyi a harkar demkoradiyyar, kuma hakan na da mahimmaci kwarai da gaske.

Kungiyar tarrayer Turai ma ta ce tana duba yiwuwar daukar mataki makamacin wanda Amurka ta dauka.

Sakataren harkokin wajen Amurka, William Hague ya ce kungiyar za ta dage wasu daga cikin takunkumin da ta kakkabawa kasar.

Ya ce zaben da aka gudanar a kasar ya nuna cewa an samu kyayyawar sauyi a kasar.

Mista Hague da Clinton sun ce suna so su ga dai gwamnatin kasar ta Burma ta saki fursunonin siyasa.

Kungiyar kasashen Yankin Asiya (ASEAN) a wani taron da ta gudanar a Cambodia ta yi kira da a dage duk takunkumin da aka sanyawa kasar a wani yunkuri na habbaka harkar demokradiyya da kuma tattalin arziki a Burma.