Kwamitin sulhu ya amince da wa'adi kan Syria

dakarun Syria
Image caption dakarun Syria

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya goyi bayan wa'adin da aka ba dakarun gwamnatin Syria na ranar Talata mai zuwa cewa su dkawo karshen hare haren da suke kai wa a kan 'yan adawa.

Kwamitin ya kuma yi kira ga Syria da ta gaggauta aiwatar da alkawarin da ta yi na janye dakarunta, da ma kwashe makamanta daga wuraran da jama'a suke sosai.

Wakilin musaman na Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar kasashen Larabawa a Syria, Kofi Annan, ya ce gwamnatin Syria ta fada masa cewa kusan an janye sojojin daga birane uku, yayin da a fili take cewa suna ci gaba da kai hare hare.

Wakilin BBC MDD ya ce Mr Annan ba shi da masu sa masa ido a Syria, dan haka da wuya ya tabbatar da ainahin abin da ke faruwa.

wakilin BBC a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya ya ce sai dai kuma Mr Annan ba shi da masu sa ido a cikin kasar ta Syria, don haka abu ne mai wuya ya iya tantance abubuwan dake faruwa.

Karin bayani