'Yan Syria na kwarara zuwa Turkiyya

Sansanin 'yan gudun hijirar Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sansanin 'yan gudun hijirar Syria

Jami'an gwamnatin Turkiyya sun ce yawan mutanan dake tserewa rikicin da ake yi a Syria ya yi matukar karuwa cikin sa'o'i ashrin da hudun da suka gabata.

Rahotanni daga daya daga cikin garuruwan dake kan iyaka, Reyhanli, sun ce kimanin 'yan Syria dubu daya sun isa Turkiyyan-wanda shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu a 'yan watannin nan.

Masu fafutuka sun ce yadda dakarun sojin Syrian ke kai hare hare kauye-kauye suna fatattakar mazauna wuraran ne ya sa adadin masu tserewar ya karu.