Shugaba Mutharika na kasar Malawi ya rasu

Shugaba Bingu wa Mutharika Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Bingu wa Mutharika na Malawi

Allah Ya yiwa Shugaban Malawi, Bingu wa Mutharika, rasuwa a sakamakon bugun zuciya, yana da shekaru saba'in da takwas.

A cikin shekara guda da ta wuce Mista Mutharika ya fuskanci matsananciyar matsin lamba a gida da waje, bayan da kasashe masu bayar da agaji suka katse taimakon da suke baiwa kasar, kuma masu sukarsa suka rika neman ya yi murabus.

Da Shugaba Mutharika ya sauka daga mukaminsa shekaru uku da suka gabata, lokacin da wa'adin mulkinsa na farko ya kare, da ya ji dadin ritaya, ganin irin namijin kokarin da ya yi a matsayinsa na shugaban kasa.

Idan aka yi la'akari da irin horon da ya samu a matsayinsa na masanin tattalin arziki, da kuma aikin da ya yi a Bankin Duniya, Mista Mutharika ya jagoranci Malawi ta samu habakar tattalin arziki na kashi tara cikin dari a kowacce shekara.

Kuma kasancewar kasarsa ba mai ci gaba sosai ba ce ta fannin tattalin arziki, Mista Mutharika ya kasance dan lelen manyan kasashen duniya masu bayar da tallafi.

Kamar yadda ya fadi a wani jawabi ga majalisar dokokin kasar a baya, “Idan har za mu iya nuna cewa za mu yi aiki tare da inganta rayuwar galibin al'ummarmu, lallai za mu iya cewa mu ma mun kawo karfi a siyance”.

Sai dai kuma farin jininsa ya dusashe matuka a wa'adin mulkinsa na biyu.

Ya yi fada da mataimakiyarsa, sannan ya

tsara yadda kaninsa Peter zai yi takarar shugabancin kasar a shekara ta 2014.

Daga nan kuma ya fara takun saka da kasashen masu bayar da tallafi, har ma ya kori jakadan Burtaniya a kasar ta Malawi bara, bayan da jakadan ya bayyana Mista Mutharika a matsayin mai kama-karya wanda baya son a soke shi.

A watan Yulin bara kuma, an yi zanga-zanga a kasar saboda hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da kuma karancin man fetur; jami'an tsaro kuma suka yi amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zangar.

A lokacin zanga zangar dai, mutane goma sha tara sun mutu.

Daga bisani ne kuma Burtaniya da Kungiyar Tarrayar Turai (EU), da Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) da kuma Bankin Duniya suka janye tallafin da suke baiwa gwamnatin Malawi.

A martanin da ya mayar, Shugaba Mutharika ya yi Allah-wadai, yana cewa janye tallafin nasu ba zai sauya komai ba, ya kuma bukaci magoya bayansa su kawar da 'yan adawa.

A matsayinsa na dan shekaru 78, rayuwar siyasar Mista Mutharika ta kare ne a wani irin yanayi.

Karin bayani