'Yan Sudan ta kudu na fuskantar kora a Sudan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan sadarwa da kakain sojin Sudan ta kudu

Kusan yan Sudan ta kudu rabin miliyan ne suke zaune a Sudan, suna zaman dar-dar ko Sudan za ta korasu zuwa kudnaci; watanni tara bayan raba kasar gida biyu.

Yan sudan ta kudun dai basu samu takardun Sudan ta kudu ba ko aiki ko kuma ma takardar izinin zama a Sudan.

Da yawansu na fargabar cewa za su bar Sudan saboda babu wata yarjejeniya akan haka.

Ranar Lahadi ne karshen wa'adin da a aka ba su don su samu takaradun da zai ba su damar zama.

Wasu yan Sudan ta Kudu na barci ido daya a bude suna jiran su samu kudin da zasu koma gida on gudun kora daga kasar Sudan.

Karin bayani