Turkiyya ta nemi taimako kan rikicin Syria

Ministan wajen Turkiyya, Ahmet Davutoglu
Image caption Ministan wajen Turkiyya, Ahmet Davutoglu

Ministan harkokin wajen Turkiyya , Ahmet Davutoglu ya nemi Majalisar Dinkin Duniya da ta taimaka wa kasar Turkiyyar domin ta iya daukar dawainiyar 'yan gudun hijiar da ke kara kwarara cikin kasar daga Syria.

Kwararar 'yan gudun hijirar ta rubanya tun bayan da gwamnatin Syria ta amince da sharuddan zaman lafiyar da ke kiran da a kawo karshen hare haren da sojoji ke kaiwa nan da goma ga watan Aprilu.

Kimanin 'yan gudun hijira dubu uku ne suka tsallaka kan iyaka suka shiga Turkiyyar, cikin sa'o'i ashirin da hudu.

Da dama daga cikin 'yan gudun hijirar na cewa ana kai hare haren bama bamai.

Mr Davutoglu ya ce halin da ake ciki a cikin kasar ta Syria da ce abin damuwa ne matuka.

Yanzu haka akwai 'yan gudun hijirar Syria su kimanin dubu hudu a kasar ta Turkiyya.

Karin bayani