An kashe mutane sama da dari a Syria

dakarun Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption dakarun Syria

Masu fafutuka a Syria sun ce, dakarun gwamnati sun kashe mutane da suka kai dari da talatin yayin jerin wasu hare-hare fadin kasar.

An bada rahotannin a kokarin kutsawa cikin garin Latamna na lardin Hama dakarun gwamnati sun ta luguden wuta.

Hotunan da aka sanya a Internet sun nanu wani wuri da ake tara gawarwaki a mota kirar a-kori-kura.

Wakilin BBC ya ce, tashin hankali ya tsananta ne a kasar ta Syria yayin da ake tunkarar wa'adin nan da ranar Talata da aka tsaida domin gwamnatin ta dakatar da kai hare-hare, da kuma janye tankokin yaki da dakaru daga wasu garuruwa.

Hukumomin Syriar sun aike da wasika Majalisar Dinkin Duniya suna cewa, wasu da ta kira 'yan ta'adda ne ke kai hare haren, tun bayan da Syriar ta amince da shirin sulhun na Mr Kofi Annan.

Karin bayani