Agajin da Kasashe masu arziki ke bayar wa ya ragu

Matsalar Fari a Afirka Hakkin mallakar hoto Oxfam
Image caption Tallafin da Kasashe masu arziki su ke baiwa Kasashe matalauta ya ragu

Agajin da Kasashen duniya suke baiwa Kasashe masu tasowa ya yi kasa a karo na farko cikin shekaru goma sha hudu

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Kasashe masu arziki suke daukar matakan tsuke bakin aljihu, biyo bayan rikicin tattalin arzikin duniya

Kungiyar hadin kan tattalin arziki da kuma cigaba ta OECD tace agajin da wadannan Kasashen suke bayarwa ya yi kasa da kashi biyu da digo bakwai cikin dari a bara, a lokacin da Kasashe matalauta ke matukar bukatar sa

Kungiyar ta OECD tace Austria da Belgium da Girka da Japan da Spain su ne Kasashen da suka fi zaftare agajin da suke baiwa Kasashen masu fama da talauci

Karin bayani