Bam ya fashe a Unguwar Tudun Wada dake birnin Jos

Sojojn Najeriya a inda wani bam ya fashe Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bam ya fashe a UnguwarTudun Wada dake birnin Jos

Rahotanni daga Jos babban birnin Jahar Filato a najeriya na cewa wani bam ya fashe a kusa da wata mashaya a Unguwar Tudun wada.

Kakakin rundunar 'yansandan Jahar Filato Mr Samuel Dabai ya tabbatar wa BBC cewa mutum guda ne ya jikkata, kuma babu wanda ya rasa ransa a tashin bam din.

Kakakin ya kara da cewar har ya zuwa yanzu ba a kama wanda ya dasa bam din ba.

Tashin bam din dai na Jos ya faru ne wasu sa'oi bayan fashewar wani bam din a Jahar Kadunan arewacin Najeriyar, inda mutane da dama su ka rasa rayukansu

Karin bayani