Korea ta Arewa na shirin harba tauraro

rokar harba tauraron dan adam Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption rokar harba tauraron dan adam

Korea ta arewa ta kai 'yan jarida na kasashen waje domin su ga abinda ta kira rokar da zata aika taurorin dan adam mai nadar bayanai zuwa sararin samaniya.

Wannan dai wani kokari ne Korea ta arewan ke yi domin gamsar da duniya cewa, shirin nukiliyarta na zaman lafiya.

Wakilin BBC da ya je wurin ya ce, an kintsa rokar da za a harba din zuwa sararin samaniya nan da wasu kwanaki.

Wakilin BBC ya ce, da wuya dai wannan mataki na Korea ta arewa ya gamsar da Amurka da kawayenta dake cewa, rokar da ake shirin harbawa, wani bangare na shirin makaman nukiliyar Korea ta arewan.

Amurka, da Japan da Koriya ta Kudu sun zargi Koriya ta Arewa da fakewa da harba tauraron dan Adam din domin gwada makami mai linzami.

Sun yi barazanar harbo tauraron dam Adam din.

Karin bayani