Toumani Toure ya sauka daga mulki

Amadou Toure Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Amadou Toure

Hambararren shugaban Mali, Amadou Toumani Toure ya bayyana sauka daga mukaminsa.

Mai shiga tsakani a rikicin Mali a madadin kasashen yammacin Afurka, wato ministan harkokin wajen Bukina Faso, Djibril Bassole ya ce, ya samu takardar yin murabus dinsa bayan wata ganawa da yayi da Amadou Toumanin Touren a Bamako, babban birnin Mali.

Murabus din Amadou Toumani Touren dai zai share fagen sauka daga kan karagar mulki na sojan da suka yi juyin mulki fiye da makonni biyu da suka gabata.

Hakan dai zai auku ne bisa tsarin shiga tsakani da kungiyar kasashen yammacin Afurka, wato ECOWAS ta yi.

Tuni kungiyar ta bada sanarwar janye takunkumin da ta kakaba wa Mali din a sakamakon juyin mulkin, wanda kasashen duniya suka yi Allah wadai da shi.

Karin bayani