Shugaba Asif Ali Zardari na ziyara a Indiya

Shugaba Asif Ali zardari na Pakistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Asif Ali zardari na Pakistan zai ziyarci wurin ibadar musulmi a Indiya

Shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, na ziyarar kwana daya wacce ba ta aiki ba zuwa Kasar Indiya .

Ziyarar wacce ita ce irin ta farko da wani shugaban Pakistan ya taba kaiwa Indiyaan cikin shekaru bakwai, na zuwa ne wasu 'yan kwanaki bayan da Indiyan ta sake zargin Kasar Pakistan da baiwa mutumin da ta ce shiya shirya hare- haren da aka kai a Mumbai a shekarar 2008 matsuguni

Mr. Zardari zai gana da Fira Ministan Kasar Indiyan Manmohan Singh, kafin ya kai ziyara zuwa wani muhimmmin wurin ibadar musulmi

Shugaban na Pakistan ya goyi bayan dage takunkumin cinikayyar da aka kakabawa Indian, saboda haka akwai fatan da ake na cewar ziyarar zata taimaka wajen inganta dangantakar tattalin arziki tsakanin Kasahen biyu

Karin bayani