Ana gudanar da zabe a lardin Aceh na Kasar Indonesia

'Yan takarar gwamna a Lardin Aceh Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zabe a lardin Aceh na Kasar Indonesia

Al'ummar lardin Aceh dake Kasar Indonesia na kada kuri'a a zabubbuka na biyu, tun lokacin da aka kulla wata yarjejeniyar zaman lafiya data kawo karshen yakin 'yan aware da aka shafe shekaru talatin ana yi.

Zaben mukamin Gwamnan Ache dai shike da matukar mahimmnci a zaben.

Gwamna mai ci yanzu haka, Irwandi Yusuf, yana fuskantar babban kalubale daga Zaini- Abdullah, wanda yake samun goyan bayan akasarin tsofaffin kungiyoyin 'yan tawaye

Hamayyar dake tsakanin 'yan takarar biyu, yasa an soma nuna damuwa, cewar za a iya zubadda jini bayan bayyana sakamakon zaben

Kasar Indonesia dai ita ce Kasar da ta fi yawan al'ummar musulmi a duniya, amma Aceh ne kadai lardin da ake aiwatar da shari'ar musulunci

Karin bayani