Omar Sulaiman zai tsaya takarar Shugabancin Kasar Masar

Magoya bayan Omar Sulaiman Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon babban jami'in leken asirin Masar, Omar Sulaiman ya shiga takarar Shugaban Kasa

Babban jami'in leken asirin tsohon Shugaban Kasar Masar Hosni Mubarak Omar Sulaiman, ya shiga takarar Shugabancin Kasar a hukumance

Hakan yasa jama'a rade- radin cewar zai samu goyan bayan manyan hafsoshin sojin Kasar.

Daya daga cikin abokanan hamayyarsa, kuma mutumin da Kungiyar Muslmin Brotherhood ta tsayar Khairat Al Shater, yace tsaida Mr. Sulaiman a matsayin dan takarar Shugaban Kasa, cin mutunci ne ga al'ummar Kasar ta Masar.

Wakiliyar BBC tace jami'an hukumar zaben Kasar sunce 'yan takara ashirin da uku ne sukai rajistar tsayawa zaben, kuma kowannensu na fatan zama Shugaban Kasa a karo na farko tun bayan hanbarar da tsohon Shugaba Hosni Mubarak.

Karin bayani