Turkiyya ta gargadi dakarun Syria

Rikicin kasar Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Talata ne wa'adin tsagaita wuta na Majalisar Dinkin Duniya zai cika

Turkiyya ta bukaci dakarun Syria da su daina harbe-harbe akan iyakar ta bayan da wasu mutaneda dama da ke wani sansanin 'yan gugdun hijira suka samu raunuka sakamakon harbe-harben.

Cikin wadanda harbe-harben suka raunata, harda wani dan Turkiyya mai yiwa 'yan gudun hijirar tafinta.

Rahotannin sun kuma ce an kashe wani dan jarida mai daukar hoto na gidan talabijin na Lebanon a kan iyakar kasar da Syria.

Daya daga masu gudun hijirar ya ce: "ai munyi gudun gara ne muka taras da zago.

Mun dauka cewa Turkiyya za ta kare mu, ga kuma irin halin da muka shiga. Da mun sani tsayawa kawai muka yi a kasar mu".

Akalla mutane 18 ne suka samu raunuka, yayin da biyu daga cikinsu suka mutu bayan an kaisu asibiti.

Masu gudun hijira dubu 25 ne suka shiga Turkiyya daga Syria tun bayan da tashin hankali ya barke a Syriar fiye da shekara guda yanzu.

Wannan lamari dai na faruwa ne a daidai lokacin da wa'adin tsagaita wuta na Majalisar Dinkin Duniya zai cika a ranar Talata.

Karin bayani