Goodluck ya kaddamar da hade ilimin boko da allo

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan

A yau Talata ne Shugaban Nijeriya Dr. Goodluck Jonathan ya kaddamar da shirin maido da ilimin karatun allo karkashin tsarin ilmi na hukuma.

Ya yi hakan ne a birnin Sokoto, dake arewacin Nijeriya, inda ya bude wata makarantar da za a rika koyar da almajirai ilmin Alkur'ani da na boko .

A watan Disamba ne dai gwamnatin Najeriya ta fara gina wasu makarantu 400 a jihohi goma sha tara na Arewacin kasar da nufin shigar da karantun almajirci cikin tsarin karatu na hukuma.

Wannan matakin a cewar gwamnatin wani yunkuri ne na magance matsalar barace-baracen da almajiran ke yi, da kuma baiwa dubban yaran damar samun ingantaccen ilmi.

To sai dai wasu masu fashin baki na ganin cewar gwamnatin na son saka hannu cikin sha'anin almajircin ne saboda tunanin cewar a makarantun almajiran ne wasu masu tayar da kayar baya a kasar ke koyon tsananin kishin addini.