Rick Santorum ya janye daga takara a Amurka

Rick Santorum Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rick Santorum, ya janye daga takara

Daya daga cikin masu son jam'iyar Republican ta tsayar da su takarar shugaban kasa a Amurka, Rick Santorum ya bayyana janyewa daga takara.

Mr Santorum ya ce a karshen mako ne shi da iyalinsa suka yanke shawarar janye takarar tasa.

Ya bada sanarwar hakan ne a jiharsa ta haihuwa, Pennsylvania.

Shi dai tsohon dan majalisar dattawa ne mai wakiltar jihar ta Pennsylvania, kuma ya fara yin fice ne, bayan da yayi nasarar ba- zata a zaben fidda gwani na jihar Iowa, cikin watan Janairu.

Sai dai daga baya yayi ta shan kaye a hannun Mitt Romney.

Janyewar tasa ta sa a yanzu shi wannan hamshakin dan kasuwa, kuma tsohon gwamna, Mitt Romney ne ake sa ran zai fafata da Barack Obama a zaben da za a gudanar na shugaban Amurka a watan Nuwamban bana.

Karin bayani