Ana ci gaba da gwabza fada a Syria

Motocin sulke a Syria
Image caption Motocin sulke a Syria

Yayinda wa'adin da aka gindaya ma sojojin gwamnatin Syria na janyewa daga garuruwa da birane ke karatowa, ana cigaba da gwabza fada a sassa dabam-dabam na kasar.

Rikicin har ma ya shiga kasashe makwabta irinsu Turkiyya da Lebanon abinda yasa ake tababar dorewar shirin na zaman lafiya.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya, Sel-Kuc Unal ya gaya ma BBC cewar, ba su dauki wannan lamari da wasa ba.

Inda ya kara da cewa suna daukar dukkan matakan da suka wajaba, ta bangaren diplomasiyya.

Haka kuma ministan harkokin wajen Syria Walid Muallem yana birnin Moscow don yin shawarwari game da tashin hankalin da ake yi a kasar a yayinda yakamata ace ana janye sojoji.