Fulani fiye da dubu 3 ne ke gudun hijira a Cross River

Nigeria
Image caption Taswirar Nigeria

A Nijeriya, Fulani Makiyaya fiye da dubu ukku ne ke zaman gudun hijira a garin Ubanliku, na Jihar Cross Rivers a kudu maso kudancin kasar.

Rahotanni na nuna cewa Fulanin Makiyayan sun yi gudun hijira ne sakamakon rikice-rikicen da suka wakana tsakaninsu da Manoma a wasu Jihohi dake arewacin kasar.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Nijeriya, wato (NEMA) ta tabbatar wa BBC kasancewar Fulani Makiyayan a Garin na Ubanliku.

Gwamnatin Jihar Cross Rivers ta ce ta aike da kayayyakin taimako ga Makiyayan kafin su samu natsuwa.

Karin bayani