Syria zata dakatar da hare hare da asubahi

Kofi Annan, wakilin kasashen duniya a Syria
Image caption Kofi Annan, wakilin kasashen duniya a Syria

Gwamnatin Syria ta bada sanarwar cewa sojojinta zasu dakatar da kai hare hare a kan 'yan tawayen kasar daga asubahin gobe Alhamis.

Wakilin kasashen duniya na musamman kan rikicin kasar Syriar Kofi Annan ya ce an sanar da shi wannan shawara da hukumomin Syriar suka yanke.

Tuni dama 'yan adawan Syrian suka ce za su mutunta yarjejeniyar, idan har dakarun gwamnati su ka janye, tare da manya-manyan makamansu.

Ba kasafai dai ake samu wakilin kasashen duniya yayi tattaki zuwa Iran a kokarin samun mafita kan rikicin wata ta yankin gabas ta tsakiya ba.

Amma ziyarar da Kofi Annan ya kai Iran, daya daga cikin kawayen Syria 'yan kalilan, alama ce dake nuna yadda yake fadi tashin bin duk wata hanya da zai iya domin ganin ya kawo kasrhen fadan tashin hankalin da ake yi a Syria.

Karin bayani