Kasar Sudan ta fice daga sasantawar da ta ke da Sudan ta Kudu

dakarun Sudan ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

dakarun Sudan ta Kudu

Gwamnatin kasar Sudan ta fice daga sasantawar da ta ke da Sudan ta Kudu, yayin da aka shiga rana ta biyu ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin kasashen biyu kan yankin Heglig dake da rijiyoyin mai.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sudan Rahamtallah Mohammed Osman ya ce ba ya jin yanayin da ake ciki zai bada damar sasantawa.

Ya ce "ta ya za ka sasanta da wanda yai ma kaka-gida a kasarka?"

Wani babban jami'i a Khartoum ya ce, Sudan ta kai kukanta ga Majalisar Dinkin Duniya da tarayyar Afirka kan abin da ta kwatanta harin ba gaira ba saban da Sudan ta Kudu ke kai mata.

Kungiyar tarayyar Afirka ta nemi Sudan ta Kudu da ta fice daga Heglig din ta kuma ce ta yi matukar damuwa kan yadda rikicin ke bazuwa.

Yaki a iyakar kasashen biyu ya sake barkewa ne a ranar Talata da rana.

Shugabannin kasashen duniya da dama sun bayyana fargabar su ta yiwuwar sake komawa yaki a tsakanin kasashen biyu, bayan wannan taho mu gama.

Yawanci dai ana ganin Heglig a matsayin yanki ne na Sudan, kodayake Sudan ta Kudu ta musanta haka.

Wakilin BBC ya ce yaki na baya bayan nan shine mafi kazancewa tun bayan da Sudan ta Kudu ta samu yancin kai a watan Yuli.