ECOWAS za ta yi taro kan rikicin Mali da Guinea Bissau

Kungiyar ECOWAS Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kungiyar ECOWAS

A yau ne tawagar Ministocin kasashen waje na kungiyar bunkasa tattalin arziki yammacin Afrika wato ECOWAS za su gana a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast.

Taron zai mai da hankali ne kan shawarwarin da aka gabatar na warware rikicin siyasar da ta dabaibaye kasashen Mali da Guinea Bissau.

Tun da farko shugabannin kasashen kungiyar ta ECOWAS a taron da suka gudanar ranar 29 ga watan Maris a Abidjan sun ce za su aike da dakarun soji matukar 'yan tawayen kasar Mali suka ki amincewa da tayin tsagaita wuta da aka yi musu domin a tattauna.

To sai dai, wasu masu sharhi kan harkokin kasa-da kasa na ganin cewa amfani da karfin soji, zai kara dagula alamura ne kawai.

Karin bayani