Tashin hankali ya ragu a Syria

annan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Assad da Kofi Annan

Rahotanni daga Syria sun ce tashin hankali yayi matukar raguwa, sakamakon yarjajeniyar dakatar da bude wutar da majalisar dinkin duniya ta taimaka wajen cimmawa - ko da yake masu fafutuka na zargin dakarun gwamnati da kaiwa fararen hula hare-hare a wurare da dama.

A cewarsu, har yanzu ana ganin sojoji da tankunan yaki da kuma manyan makamai a ciki da kuma a kewayen wurare masu cunkoson jama'a.

Gidan talabijin din Syria ya ce, wani jami'in soja ya hallaka, kuma wasu sojojin ashirin da hudu sun jikkata, bayan tashin wani bam da aka dana a gefen hanya, wanda gidan talabijin din ya ce yin 'yan ta'adda ne.

Kasar China ta nuna fatan cewa gwamnatin Syria za ta cigaba da daukar matakai na zahiri, wajen kawo goyon baya ga shirin Kofi Annan na samar da zaman lafiya.

Karin bayani