Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Syria

Kofi Annan
Image caption Kofi Annan

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki tsakanin gwamnati da yan adawa a Syria, duk da rashin kwarin gwiwar da wasu suka nuna.

Gwamnatin kasar ta ce za ta yi aiki da yarjeneiyar, to amma za ta mai da martani idan wadanda take kira yan taadda sun kai mata hari.

Kungiyoyin yan adawa, sun bayyana rashin kwarin gwiwar su game da alwashin da gwamnatin da dauka na janye dakarun ta da tankokin yaki a manyan biranen kasar, wanda suka ce babu alamar yiwuwar hakan.

Su ma kasashen yammacin duniya sun ce izuwa yanzu Damashka ba ta mutunta daukacin shirin tsagaita wutar ba.

Masu goyon bayan Syria sun jaddada cewar, akwai bukatar su ma yan adawa su dakatar da hare haren da suke kaiwa.